logo

HAUSA

Wani jirgin sama ya fada tafkin Victoria na kasar Tanzania

2022-11-06 16:57:10 CMG Hausa

Rahotanni daga kasar Tanzaniya, na cewa wani jirgi mallakin kamfanin sufuri na Precision Air, ya yi hadari, inda ya fada tafkin Victoria dake yankin Bukoba na jihar Kagera.

Kafofin watsa labaran kasar sun ce ana shirin fara gudanar da ayyukan ceton wadanda ibtila’in ya rutsa da su. (Saminu Alhassan)