logo

HAUSA

Dan kunar bakin wake ya hallaka mutane 15 a kofar wani sansanin sojoji dake birnin Mogadishu

2022-11-06 16:54:32 CMG Hausa

Rahotanni daga kasar Somaliya, na cewa da yammacin jiya Asabar, wani dan kunar bakin wake ya hallaka kan sa, tare da wasu mutanen a kalla 15, lokacin da ya tada wani Bam dake jikin sa, a mashigar wani sansanin horas da sojoji dake kudancin birnin Mogadishu fadar mulkin kasar.

Tuni dai kungiyar masu tsattsauran ra’ayin Islama ta Al-Shabab, ta dauki alhakin kaddamar da harin. Kafin hakan, da yammacin ranar Alhamis, sojojin gwamnatin Somaliya, masu samun goyon bayan mayakan sa kai dake kasar, sun hallaka sama da mayakan al-Shabab 100, yayin wani hari da suka kaddamar a wani kauye dake jihar Hiran ta tsakiyar kasar.

Wannan lamari na zuwa ne mako guda, bayan harin tagwayen bama-bamai cikin wasu motoci 2, da aka nufi ma’aikatar ilimin kasar da su, wanda ya sabbaba kisan a kalla mutane 100, tare da jikkata sama da mutane 300.   (Saminu Alhassan)