logo

HAUSA

Jawabin Xi Jinping a bikin CIIE ya karfafa gwiwar wasu tsoffin mahalarta bikin

2022-11-06 19:53:30 CMG Hausa

A daren ranar Jumma’a 4 ga wata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ta kafar bidiyo, ya halarci bikin kaddamar da baje-kolin kayayyakin kasa da kasa da ake shigowa da su kasar Sin ko kuma CIIE karo na biyar wanda ake yi a birnin Shanghai, inda ya gabatar da wani muhimmin jawabi. Shugabannin kamfanonin kasashen waje da dama wadanda suka taba halartar bukukuwan CIIE da suka gabata, sun jinjinawa jawabin Xi, saboda alkawarinsa na fadada bude kofar kasarsa ga kasashen waje, da fatan more damammakin ci gaban kasar Sin mai inganci.

Mista Homma Tetsuro, mataimakin shugaban kamfanin Panasonic Holding Co. na kasar Japan, wanda yake halartar bikin CIIE har shekaru biyar a jere ya bayyana cewa, ya samu karfin gwiwa sosai daga jawabin shugaba Xi, saboda kalamansa dake nuna aniyar kasar Sin, ta nacewa bin hanyar bude kofa ga kasashen ketare, da samar da ci gaba mai inganci ta hanyar bude kofar kasa.

Shi ma a nasa bangaren, wani babban jami’in kwamitin kula da huldar tattalin arziki da kasashen waje na kasar Türkiye, Murat Kolbasi cewa ya yi, tun bikin CIIE karo na farko ya zuwa yanzu, akwai kyawawan kamfanonin kasarsa kusan 100 da suka halarci bikin, kuma darajar kayayyakin da kasar ta fitar zuwa kasar Sin ta hanyar halartar bikin, ta zarce dala miliyan 500. (Murtala Zhang)