logo

HAUSA

Duniya za ta more manyan damammaki uku daga kasar Sin mai bude kofarta ga kasashen waje

2022-11-06 16:13:28 CMG Hausa

A daren ranar Jumma’a 4 ga wata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ta kafar bidiyo, ya halarci bikin kaddamar da baje-kolin kayayyakin kasa da kasa da ake shigowa da su kasar Sin ko kuma CIIE karo na biyar wanda ake yi a birnin Shanghai, inda ya yi jawabin dake jaddada cewa, kasarsa za ta taimakawa kasa da kasa, more damammakin ci gaba tare. Xi ya ce, “Ya dace mu kara bude kofarmu, don daidaita matsalolin ci gaba, da fadada hadin-gwiwa, da kara karfin yin kirkire-kirkire, da kuma samar da ci gaba tare, ta yadda za’a kara dunkule tattalin arzikin duniya baki daya, da samar da ci gaba ga kasa da kasa, don kara amfanar al’ummominsu cikin adalci”.

A shekaru biyar da suka wuce, shugaba Xi ya sanar da gudanar da bikin CIIE, da zummar fadada bude kofar kasar Sin, ta yadda babbar kasuwar kasar za ta zama babban zarafi ga duk duniya baki daya. Kididdigar ta nuna cewa, a wajen bukukuwan CIIE hudu da suka gabata, adadin kayayyakin da aka baje kolinsu, sun kai dubu 270, kuma jimillar darajar yarjeniyoyin da aka daddale ta zarce dala biliyan 270, inda aka bullo da sabbin hajoji, da fasahohi, da hidimomi da yawansu ya wuce 1500.

Bikin CIIE, tamkar dandali ne ga kasar Sin, na kafa sabon tsarin samar da ci gaba, da fadada bude kofarta ga kasashen ketare, inda sassan kasa da kasa za su ci gajiya tare.

Baje kolin CIIE na bana, kasaitaccen bikin kasa da kasa ne na farko da kasar Sin ta gudanar, tun bayan da ta kira babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis karo na 20, wanda ya samu halartar kasashe da yankuna, da kungiyoyin kasa da kasa 145, gami da kamfanoni 284 dake sahun gaba a duniya.

Rahoton babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis karo na 20 ya jaddada cewa, kasar Sin za ta nace ga bin manufar bude kofarta ga kasashen waje, tare da cin moriya tare da kasashe daban-daban, ta yadda duniya za ta amfani sabon ci gaban kasar Sin.

A jawabin shugaba Xi, ya sake nanata cewa, kasarsa za ta taimakawa kasashe da bangarori daban-daban, ta yadda za su more damamakin da suka shafi babbar kasuwar kasar, da manufar bude kofa ga kasashen waje, da habaka hadin-gwiwa tsakanin kasa da kasa. Manazarta na ganin cewa, damammakin uku, za su sanya babban kuzari ga tattalin arzikin duniya, wanda a yanzu haka yake murmurewa daga mawuyacin hali. (Murtala Zhang)