logo

HAUSA

Sin ta kalubalanci Canada game da umarnin amshe ikon zuba jari na wasu kamfanonin hakar ma’adanai

2022-11-06 16:50:56 CMG Hausa

Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta bayyana matukar rashin amincewa, da umarnin gwamnatin kasar Canada, na karbe ikon wasu kamfanonin Sin na zuba jari a fannin hakar ma’adanai, ta hanyar fakewa da batun tsaron kasa.

A ranar Laraba ne gwamnatin Canada, ta umarci kamfanonin Sinomine da Chengze Lithium na Hong Kong, da kamfanin Zangge na birnin Chengdu, da su mika ikon su na zuba jari ga wasu kamfanonin hakar sinadarin lithium na kasar ta Canada. Gwamnatin Canadan ta ce batun tsaron kasa ne ya sa ta daukar wannan mataki.

Wata sanarwa da ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta fitar game da hakan,  ta ce Sin da Canada muhimman kasashe ne a fannin hada hadar hakar ma’adanai, sai dai kuma matakin da gwamnatin Canada ta dauka, na amfani da batun tsaro, domin tankwara tsarin hadin gwiwar cinikayya da zuba jari tsakanin kamfanonin kasashen biyu sam bai dace ba.

Hakan a cewar sanarwar, ya sabawa tsarin cudanyar kasuwanni, da hada hadar tattalin arziki tsakanin kasa da kasa, da ma sauran dokokin kasuwanci, kuma ko alama Sin ba za ta amince da hakan ba.(Saminu Alhassan)