logo

HAUSA

Sabon ci gaban Sin ya samar wa Afirka sabuwar dama

2022-11-05 15:19:33 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwararsa ta kasar Tanzaniya dake ziyarar aiki a kasar Sin Samia Suluhu Hassan a birnin Beijing, fadar mulkin kasar a ranar 3 ga wannan wata da muke ciki, inda suka sanar da cewa, za su daga matsayin huldar hadin gwiwa ta sada zumunta bisa manyan tsare-tsare daga duk fannoni dake tsakanin kasashen biyu wato Sin da Tanzaniya zuwa wani sabon mataki, haka kuma sun cimma matsaya kan batutuwa da dama, ciki har da kiyaye cudanya da tattaunawa, da habaka hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da sauransu.

Ban da haka, shugabannin biyu sun fitar da hadaddiyar sanarwa, tare kuma da daddale takardun hadin gwiwa da dama, wadannan suka kara kuzari kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Tanzaniya, da ma tsakanin Sin da Afirka a sabon zamanin da ake ciki yanzu.

Shugaba Hassan, ita ce shugabar kasashen Afirka ta farko wadda ta kawo ziyara kasar Sin, tun bayan da aka kammala babban taron wakilan JKS karo na 20, lamarin da ya nuna cewa, akwai daddaden zumunci tsakanin kasar Sin da kasar ta Tanzaniya.

Yayin tattaunawar da suka yi, shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin tana son samar da sabuwar damar raya kasa ga kasashen Afirka, kuma tana son kara taka rawa wajen nacewa kan manyan ka’idojin tafiyar da harkokin kasa da kasa, da tabbatar da shawarwarin raya duniya, da daga matsayin kasashe masu tasowa a cikin harkokin kasa da kasa, da kuma ingiza gina kyakkyawar makomar bai daya ga daukacin bil Adama. Ana iya cewa, kalaman Xi sun bayyana aniyar kasar Sin ta kara habaka hadin gwiwar dake tsakaninta da Afirka. (Jamila)