logo

HAUSA

Xi ya gana da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz

2022-11-04 13:59:38 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana a yau Juma’a, da shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, a nan birnin Beijing.

Olaf Scholz, wanda ke ziyara a kasar Sin, shi ne shugba na farko daga Turai da ya ziyarci kasar Sin, bayan kammala babban taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin.

Yayin ganawar, Xi Jinping ya ce, ziyarar za ta karfafa fahimtar juna da aminci tsakanin bangarorin biyu, baya ga zurfafa hadin gwiwarsu a bangarori da dama. Haka zalika, za ta ba bangarorin biyu damar shirya yadda za su habaka dangantakarsu a nan gaba.

Da yake bayyana yanayi mai sarkakiya da duniya take ciki, shugaba Xi ya ce a matsayinsu na manyan kasashe masu tasiri, akwai bukatar Sin da Jamus, su hada hannu a wannan lokaci na sauyi da rashin tabbas, su bayar da karin gudunmuwa ga zaman lafiya da ci gaban duniya. (Fa’iza Mustapha)