logo

HAUSA

Kudin shiga daga mai a Nijeriya ya ragu da dalar biliyan 12.6 a farkon watanni tara na bana

2022-11-04 13:52:02 CMG Hausa

Jaridar “The Guardian” ta Nijeriya, ta ce tun daga watan Janairu zuwa Satumba na bana, kudin shigar da Nijeriya ke samu daga danyen mai ya ragu da dalar biliyan 12.6, idan an kwatanta da makamancin lokaci na bara, sakamakon raguwar danyen man da kasar ke hakowa.

Jaridar ta kara da cewa, a ’yan makwanni baya ne gwamnatin tarayyar Nijeriyar ta fitar da kasafin kudi na shekarar 2023 da ya kai Naira triliyan 20.5, wato kusan dalar Amurka biliyan 47.3.

Dalilin da ya sa raguwar kudin shiga ya kai fiye da dalar biliyan 12.6 daga man fetur shi ne, raguwar man fetur da take hakowa. Wannan adadi ya kai fiye da kwata na yawan kasafin kudin kasar na shekara mai zuwa.

An ce, muhimman dalilan da suka haddasa raguwar fitar da man fetur a Nijeriya a bana su ne koma bayan manyan ababen more rayuwa, da laifin satar man fetur din da kasar ke fuskanta. (Safiyah Ma)