logo

HAUSA

Sanarwa kan yadda ake tafiyar da al’amura a tekun kudancin Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin

2022-11-04 20:07:28 CMG Hausa

A bana ne, aka cika shekaru 20 da sanya hannu kan sanarwa kan yadda bangarorin da abin ya shafa ke gudanar da al’amura a tekun kudancin kasar Sin. A yayin taron manema labarai na yau da kullum Jumma’ar nan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, sanya hannu da ma aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla game da tekun kudancin kasar Sin, ya karfafa amincewa da juna a siyasance tsakanin kasar Sin da kasashen ASEAN, da inganta yin shawarwari da hadin gwiwa game da tekun, ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen wanzar da zaman lafya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin, da samar da yanayi mai kyau a yankin, don raya alaka tsakanin kasar Sin da kasashen kudu maso gabashin Asiya. (Ibrahim)