logo

HAUSA

Firaministan Sin zai halarci taron shugabannin hadin gwiwar kasashen gabashin Asiya tare da kai ziyarar aiki a Cambodia

2022-11-04 19:04:01 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya sanar a yau Jumma’a cewa, bisa gayyatar takwaransa na kasar Cambodia Techo Hun Sen, firaministan kasar Sin Li Keqiang, zai halarci taron kolin Sin da kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya ko (ASEAN) karo na 25, da taron kolin ASEAN+3 karo na 25 da taron kolin kasashen gabashin Asiya karo na 17, da za a gudana a Cambodia daga ranar 8 zuwa 13 ga watan Nuwanban da muke ciki, tare da kai ziyarar aiki a kasar ta Cambodia. (Ibrahim)