logo

HAUSA

Hukumomin lafiya a Najeriya sun yi kira ga al’ummar kasar su karbi rigakafin COVID-19

2022-11-04 11:05:41 CMG Hausa

Hukumomin lafiya a Najeriya sun yi kira ga al’ummar kasar, da su karbi rigakafin cutar COVID-19, domin karfafa garkuwar jikinsu, a gabar da ake fuskantar karin hadarin barkewar annobar.

Da yake tsokaci game da hakan, yayin taron yini daya na nazarin halin da ake ciki game da rigakafin cutar a birnin Abuja fadar mulkin kasar, shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko(NPHCDA) na kasar Faisal Shuaib, ya ce har yanzu wannan cuta na ci gaba da bazuwa, don haka ya kamata dukkanin ‘yan kasar su karbi alluran rigakafinta.

Shugaban na NPHCDA, ya ce bisa sabbin alkaluman hukumar, ya zuwa ranar Talata, kaso 44.6 bisa dari na jimillar ‘yan kasar da ya dace su karbi rigakafin ne suka yi cikakken rigakafin, yayin da kaso 55.6 bisa dari na rukunin suka karbi zagayen farko na rigakafin.

Shuaib ya ce fatan su shi ne, yiwa kaso 70 bisa dari na ‘yan kasar rigakafin na COVID-19 nan da watan Disamba dake tafe.  (Saminu Alhassan)