logo

HAUSA

Kasar Sin ta fitar da takardar bayani game da tsarin taurarin dan adam na BeiDou

2022-11-04 11:44:43 CMG Hausa

Kasar Sin ta fitar da takardar bayani game da tsarin taurarin dan adam mai samar da hidimar taswira na BeiDou na kasar, a yau Juma’a.

Takardar mai taken “Tsarin taurarin dan Adam na BeiDou mai hidimar taswira a sabon zamani” ta ce an fasalta taurarin zuwa mai tsarin taswira da ya kai mizanin kasa da kasa. Haka kuma, ta gabatar da shirin kasar na sake kyautata tsarin taurarin ta hanyar inganta ayyukansa, da inganta ayyukan samar da ci gaba mai dorewa ta hanyar amfani da taurarin da daukaka tsarin jagorancinsa cikin shekaru masu zuwa.

A cewar takardar, an sadaukar da tsarin taurarin ne ga duniya baki daya, kuma kasar Sin za ta kara hada hannu da kasa da kasa, domin kyautata hadin gwiwa da dacewar tsarin taurarin BeiDou da sauran tsarukan taurarin dan adam masu bada hidimar taswira na duniya.

Haka kuma, a shirye kasar Sin take ta samar da cikakken tsari mai bayar da bayanai a ko’ina, a kowanne lokaci, wanda ya hada bangarori daban-daban, da bayar da karin hidima, kuma mai karin fasahohi a tsarukan BeiDou da na sauran tsarukan bayar da taswira a nan gaba.

Har ila yau, kasar Sin ta shirya yayata nasarorinta na samar da taurarin BeiDou, kuma za ta hada hannu da sauran kasashe wajen inganta samar da tsarukan taurarin bayar da hidimar taswira da kuma kara bayar da gudunmawa wajen gina al’ummar duniya mai makoma ta bai daya. (Faeza Mustapha)