Beidou na kasar Sin ya zama Beidou na duniya
2022-11-04 20:51:36 CMG Hausa
Na yi imanin cewa, tsarin Beidou zai ba da gudummawa ga ci gaban kasashen duniya, musamman ma yadda tsarin zai taimakawa kasashe masu tasowa, wadanda ke fadi tashin cimma burin kudororin ci gaba mai dorewa. A kwanakin nan ne, babban taron MDD na 16 ya gudanar da taron kwamitin kasa da kasa game da tsarin zirga-zirgar tauraron dan-Adam mai samar da hidimar taswira a Abu Dhabi na hadaddiyar daular Larabawa, kuma wakilan kasar Pakistan da suka halarci taron sun bayyana cewa, takardar bayanin da kasar Sin ta fitar game da tsarin Beidou na kasar a sabon zamani a yau, ta nuna cikakken goyon baya kan wannan batu.
Takardar bayanin ta yi cikakken nazari kan raya tsarin Beidou na kasar Sin, kana ta nuna cewa, tun lokacin da tsarin na Beidou ya shiga sabon zamani, ya samar da sabbin fasahohi na hidima da sabbin ci gaban masana’antu. (Ibrahim)