logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya gana da shugabar kasar Tanzania

2022-11-04 10:14:44 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da shugabar kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan, wadda ke ziyarar aiki a kasar Sin. Yayin zantawar tasu a jiya Alhamis, Li ya jinjinawa kyakkyawar alakar dake tsakanin Sin da Tanzania.

Ya ce yayin taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin(JKS) karo na 20, an fidda ingantaccen tsarin bunkasa ci gaban kasar Sin a shekaru dake tafe, kuma Sin za ta ci gaba da daga matsayin bude kofar ta ga duniya.

Kaza lika firaministan na Sin ya bayyana aniyar kasar Sin, ta fadada shigo da hajoji daga Tanzania, da karfafawa kamfanonin kasar gwiwar kara zuba jari a Tanzania, yana kuma fatan mahukuntan Tanzania za su ba da hadin gwiwar da ya wajaba domin cimma nasarar hakan.

A bangaren alakar Sin da Afrika kuwa, Li ya ce kasar sa a shirye take ta yi aiki tare da sauran kasashen Afirka bisa tushen gaskiya da daidato, da kara dinkewa da amincewa da juna, a turbar wanzar da ci gaba da tafiya tare.

A nata bangare kuwa, shugaba Samia Hassan godewa kasar Sin ta yi, bisa irin goyon baya da taimakon da take baiwa kasar ta cikin tsawon shekaru, tana mai alkawarta aniyar Tanzania, ta aiwatar da sakamakon da aka cimma, karkashin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC, da ingiza hadin gwiwar cinikayya, da zuba jari, da harkokin noma da kiwon kifi, da samar da ababen more rayuwa, da musaya tsakanin al’ummun kasashen biyu.  (Saminu Alhassan)