logo

HAUSA

Shugaban Saliyo ya yabawa na’urorin aikin gona da Sin ta ba kasar kyauta

2022-11-03 19:35:21 CMG HAUSA

 

Ran 1 ga wata, an yi bikin mikawa kasar Saliyo na’urorin aikin gona da Sin ta kera a birnin Freetown hedkwatar kasar. A jawabin da ya gabatar shugaban kasar Julius Maada Bio ya bayyana cewa, wadannan na’urorin za su taimakawa kasar wajen zamanintar da aikin gona da daga matsayin kasar a fannin samar da hatsi da kanta. Ya ce Saliyo za ta ci gaba da zurfafa hadin kai da kasar Sin a dukkan fannoni a kokarin ingiza samun ci gaba mai armashi. (Amina Xu)