logo

HAUSA

Wang Yi ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo ga dandalin hadin kai da daidaita harkokin teku na shekarar 2022

2022-11-03 19:41:37 CMG HAUSA

 

Yau Alhamis, an bude dandalin hadin kai da daidaita harkokin teku na shekarar 2022, inda ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.

Wang Yi ya nuna cewa, Sin na fatan hada kai da kasashen duniya, karkashin ruhin kafa kyakkyawar makomar sararin teku baki daya da Xi Jinping ya gabatar, don tabbatar da bunkasuwa da kuma tsaron teku, da ingiza hadin kai wajen daidaita harkokin teku.

Ya kuma gabatar da shawarwari guda 3. Na farko magance rikice-rikice cikin lumana a kan teku da hadin kan kasa da kasa don tinkarar kalubaloli tare, da nuna adawa da nuna karfin tuwo kan wannan fanni. Na biyu gaggauta tuntubar juna a wannan fanni, ta yadda za a raya da kuma kiyaye teku tare. Na uku, nacewa ga gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban da yin hakuri da juna da sulhuntawa, da kariyaye dokokin teku bisa tushen dokokin kasa da kasa, ta yadda za a daidaita harkokin teku cikin hadin kai. (Amina Xu)