logo

HAUSA

Kammala Aikin Tashar Ruwa Mai Zurfi Ta Lagos Zai Ingiza Bunkasar Tattalin Arzikin Najeriya

2022-11-03 17:28:57 CMG HAUSA

DAGA Saminu Hassan

A farkon makon nan ne kamfanin gine-gine na CHEC na kasar Sin, ya mikawa mahukuntan Najeriya aikin ginin tashar ruwa mai zurfi da ya kammala, a yankin Lekki na jihar Lagos dake kudu maso yammcin kasar.

Kwararru da dama na ganin kammala wannan gagarumin aiki a Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriya, zai ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar baki daya. Nasarar kammalar wannan aiki daya ne daga hanyoyin da Najeriya ke morar hadin gwiwarta da kasar Sin, karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”.

A matsayinta na mafi girma a Najeriya, kuma daya daga mafiya girma a Afirka, tashar ruwa mai zurfi ta Lekki, za ta bunkasa hada-hadar shige da ficen hajoji da yawansu zai kai kwantainoni miliyan 1.2 a duk shekara, tare da samarwa kasar karin kudaden shiga ta hanyar haraji da sauransu, kana Najeriyar za ta mori damammakin jawo jarin waje a fannoni daban daban.

Ko shakka babu, wannan tashar ruwa za ta amfani tattalin arziki Najeriya, da ma sauran kasashen dake tsakiya da yammacin nahiyar Afirka. Kaza lika tashar za ta samar da guraben ayyukan yi na kai tsaye kusan 200,000, da sauran guraben da ba na kai tsaye ba.

Wannan muhimmin aiki da makamantasa da kasar Sin ke tallafawa wajen samar da kudaden gudanar da su a Najeriya, da sauran kasashen Afirka, na kara shaida irin kyawawan manufofin dake kunshe cikin manufar Sin, ta tallafawa ci gaban kasashe masu tasowa, da burin kasar na bunkasa hadin gwiwa da kasashen Afirka a dukkanin fannoni, tare da samar da al’ummar duniya mai makomar bai daya ta fannin ci gaba.