logo

HAUSA

Hadin gwiwar Sin da Afirka na samar da fa’ida a zahiri ga jama’ar Afirka

2022-11-03 19:21:16 CMG Hausa

Yau ne, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya shirya taron manema labaran da aka saba gudanarwa. Kuma wani dan jarida ya gabatar da tambaya cewa, a kwanakin nan, wani binciken jin ra’ayin jama’a da wata hukumar jin ra’ayin jama’a ta kasar Burtaniya da ake kira YouGov ta yi, ya nuna cewa, a shekarun baya, al’ummar Afirka sun kara nuna sha’awarsu ga kasar Sin. Adadin ‘yan kasashen Najeriya da Kenya da Afirka ta kudu da Masar da aka zanta da su, wadanda ke ganin kasar Sin tana da matukar tasiri kan harkoki na kasa da kasa, ya kai kaso 83 cikin 100 da kaso 82 da 61 da kuma kaso 57 cikin 100 bi da bi, karuwar kaso 15 da kaso 24 da kaso 13 da kaso 10 cikin 100 bi da bi kan na shekarar da ta gabata. Shin mene ne ra’ayinka kan wannan batu?

Zhao Lijian ya ba da amsa cewa, sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’ar da ka ambata, ya sake tabbatar da cewa, alakar Sin da Afirka, ta kawo wa jama’ar Afirka alheri a zahiri, kuma jama’ar Afirka sun yi maraba da ma na’am da su. (Ibrahim)