logo

HAUSA

Hadin gwiwar Sin da Pakistan mai karfi ta haifar da sabbin sakamako

2022-11-03 19:28:58 CMG Hausa

Firaministan kasar Pakistan dake ziyara a kasar Sin Shahbaz Sharif, ya bayyana cewa, Sin da Pakistan abokai ne na kwarai, kuma abokan hulda, kana ‘yan uwa ne na gari.

Ya kara da cewa, zurfafa alaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni tsakanin Sin da Pakistan, shi ne tushen manufofin kasashen waje na Pakistan, da kuma matsayar da dukkan sassa na al’umma suka amince da su.

A nasa bangare, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yaba da kawance mai karfi dake tsakanin Sin da Pakistan, yana mai cewa, kasar Sin na fatan inganta matsayin hadin gwiwarta bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni da Pakistan. (Ibrahim)