logo

HAUSA

’Yan sanda a jihar Katsina sun tabbatar da sace wasu yara 21 a karamar hukumar Faskari

2022-11-03 10:58:53 CMG Hausa

 

Rundunar ’yan sanda a jihar Katsina dake arewa maso yammacin Najeriya, ta ce wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da wasu yara su 21 dake aiki a wata gona, a kauyen Kampani Mailafiya dake karamar hukumar Faskari dake jihar.

Kakakin ’yan sandan jiyar Gambo Isah, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, ’yan bindigar sun kutsa gonar a ranar Lahadi, inda suka tasa keyar yaran dake aiki a gonar zuwa daji.

Isah ya ce yaran da aka sace su 21, hudu daga cikin su ne kadai maza, sauran duk mata ne, suna kuma tsakanin shekaru 15 zuwa 19 da haihuwa. Jami’in ya ce tuni barayin dajin suka fara tuntubar dangin yaran domin neman kudin fansa.

Rundunar ’yan sandan ta ce kafin sace yaran, ’yan bindigar sun amince da karbar kudade daga manoman kauyen, domin kyale su su gudanar da ayyukan gona ba tare da wata barazana ba.

Isah ya ce jim kadan da jin labarin sacen yaran, ’yan sanda sun shiga farautar ’yan bindigar domin kubutar da yaran.  (Saminu Alhassan)