logo

HAUSA

Xi Jinping ya gana da shugabar Tanzaniya

2022-11-03 20:23:21 CMG Hausa

Da yammacin yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna da takwararsa ta kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, wadda ta zo kasar Sin don ziyarar aiki. Shugabannin biyu sun sanar da daga matsayin huldar dake tsakanin kasashensu wato Sin da Tanzaniya zuwa wani babban kawancen hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare. (Ibrahim)