logo

HAUSA

Moussa Faki Mahamat ya yi kira da a shigar da matasa cikin harkokin ci gaba yayin da ake bikin ranar matasa ta nahiyar

2022-11-02 10:35:15 CMG Hausa

Shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka ta AU Moussa Faki Mahamat, ya yi kira da a fadada shigar da matasa cikin harkokin bunkasa Afirka. Mahamat ya yi kiran ne albarkacin ranar matasan Afirka, da ake bikinta a ranar 1 ga watan Nuwamban kowace shekara.

Babban jami’in na AU, ya ce ana gudanar da wannan biki ne duba da muhimmancin da jagororin Afirka ke dorawa kan ci gaban matasa, kamar yadda hakan ke kunshe cikin takaitaccen kundin bayani game da tanaje-tanajen da kungiyar ta yiwa matasan nahiyar, a matsayinsu na rukunin mutanen da kundin ya bayyana da babbar kadarar nahiyar.

Mr. Mahamat ya kara da cewa, akwai bukatar kawar da dukkanin shingaye dake tarnaki ga ci gaban matasan Afirka, musamman ta hanyar wayar da kai. Kaza lika ya yi fatan ganin matasan nahiyar sun kara azama, wajen shiga a dama da su a sabon yanayin ci gaban duniya, bisa tanadin da kungiyar ta AU ta yiwa matasa a shekarar 2013, cikin ajandar ci gaban nahiyarta nan da shekarar 2063.

Daga nan sai ya jaddada cewa, tarin kalubalen dake addabar matasan Afirka na jefa su cikin yanayi na rashin gamsuwa da kansu, da karaya dame da makomar su, da ta kasashensu, da ma makomar nahiyar baki daya. (Saminu Alhassan)