logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya gana da firaministan kasar Pakistan

2022-11-02 15:49:31 CMG Hausa

 

Da safiyar yau Laraba ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya gana da firaministan kasar Pakistan Muhammad Shahbaz Sharif, wanda ke ziyarar aiki a Beijing.

A yayin ganawar tasu, shugaba Xi ya nuna cewa, kasashen Sin da Pakistan, aminai ne kuma ’yan uwa. A shekarun baya-bayan nan, suna mara wa juna baya, don samun ci gaba yayin da ake fuskantar sauye-sauye a duniya, lamarin da ya nuna dankon zumunci a tsakaninsu. Har kullum Sin na ba da muhimmanci kan raya huldar da Pakistan, yayin da take mu’amala da kasashe masu makwabta. Ya ce Sin tana son daga matsayin hadin gwiwarsu bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, da gaggauta raya kyakkyawar makomar kasashen 2 a sabon zamani, a kokarin kara sabon kuzari na bunkasar huldar abokantaka a tsakanin kasashen 2 daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare.

A nasa bangare, Muhammad Shahbaz Sharif ya ce, a shekaru 10 da suka wuce, a karkashin nagartaccen shugabancin Xi Jinping, kasar Sin ta samu gagaruman nasarorin ci gaba, ta kuma tsaya tsayin daka kan kasancewar bangarori daban daban a duniya, da kara azama kan hadin gwiwar sassa daban daban, kana ta ba da muhimmiyar gudunmmawa wajen kiyaye zaman lafiya da bunkasuwa a duniya. Don haka duniya na bukatar kasar Sin. Kuma ba wanda zai iya dakile ci gaban kasar Sin, da kuma mayar da ita saniyar ware ba.

Haka zalika, a cewar firaministan Pakistan, kasarsa na bin “manufar kasar Sin daya tak a duniya”, tana mara wa kasar Sin baya a batutuwan Taiwan, Xinjiang, Hong Kong da sauran batutuwan da ke shafar babbar moriyarta. Ya ce Pakistan tana fatan koyon fasahohin kasar Sin na tafiyar da harkokin kasa, za ta kuma tsaya da kafaffunta, kana za ta zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin a sassa daban daban, a kokarin samun ci gaba, wanda shi ne manufar Pakistan a nan gaba, kuma hanya ce daya tak da za ta bi. (Tasallah Yuan)