logo

HAUSA

Sin da Pakistan sun sanya hannu kan yarjejeniytar fahimtar juna game da amfani da RMB a Pakistan

2022-11-02 20:42:00 CMG Hausa

Babban bankin kasar Sin ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da bankin kasar Pakistan, domin bullo da wani shiri na amfani da kudin kasar Sin wato RMB a kasar Pakistan

Wata sanarwa da babban bankin al’umma na kasar Sin ya wallafa a shafinsa na Intanet, ta bayyana cewa, wadannan tsare-tsare, za su taimakawa kamfanoni da cibiyoyin hada-hadar kudi na kasashen biyu, gudanar da hada-hadar cinikayya tsakaninsu, ta hanyar amfani da RMB. (Ibrahim)