logo

HAUSA

Xi Jinping ya aike da sakon murnar bude taron shugabannin kawancen kasashen Larabawa

2022-11-02 10:55:04 CMG Hausa

A jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sako ga shugaban kasar Aljeriya, kuma shugaban karba-karba na kungiyar kawancen kasashen Larabawa Abdelmajid Tebboune, don taya shi murnar kaddamar da taron shugabannin kawancen kasashen Larabawa karo na 31.

Cikin sakon na sa, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kawancen kasashen Larabawa ya dukufa wajen karfafa hadin kan kasashen Larabawa, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya, ya kuma yi namijin kokarin kiyaye cudanyar kasa da kasa, da ma moriyar kasashe masu tasowa. Xi Jinping ya kuma yabawa Aljeriya, game da yadda take kiyaye hadin kan kasashen Larabawa, da ma halastaccen hakkin kasashe masu tasowa.

Xi Jinping ya jaddada cewa, cikin‘yan shekarun baya-bayan nan, Sin da kasashen Larabawa, sun cimma gagaruman nasarori a hadin gwiwarsu ta fannoni daban daban. Kaza lika kasar Sin na fatan ci gaba da goyon baya, da fadada hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Larabawa, ta yadda za su rungumi makomar bai daya, da ma samar da gudummawarsu, wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya. (Lubabatu)