logo

HAUSA

Cibiyar “Africa CDC” za ta zamo muhimmiyar kyautar Sin ga nahiyar Afirka

2022-11-02 11:04:51 CMG Hausa

Tsohon jakadan kasar Habasha a MDD Teruneh Zenna, ya ce cibiyar kandagarki da yaki da cututtuka ta Afirka ko “Africa CDC”, wadda kasar Sin ke samar da tallafin ginawa, za ta kasance karin kyautar Sin ga nahiyar Afirka.

Yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Mr. Zenna ya ce baya ga samar da kudaden aikin, kasar Sin din ce kuma ke aiwatar da ginin cibiyar, wadda za ta kunshi dukkanin kayayyakin aiki da ake bukata, na inganta bincike da habaka harkar kiwon lafiya a Afirka.

Zenna ya kara da cewa, ta amfani da helkwatar AU a matsayin cibiyar ba da umarni, AUn za ta taimakawa kasashe mambobin ta wajen karfafa kwarewarsu a fannin gaggauta ganowa, da shawo kan barkewar cututtuka masu hadari, kamar cutar Ebola, da COVID-19, da zazzabin shawara da dai sauran su.

Tsohon jakadan ya ce kari kan haka, cibiyar za ta zamo wani dandali da kwararrun masana kiwon lafiya na Sin, za su rika taimakawa takwarorin su na Afirka, da dabarun karfafa sanin makamar aiki a fannin yaki da annoba da ka iya bulla a nan gaba.

An fara ginin cibiyar “Africa CDC” ne tun a watan Disambar shekarar 2020 a birnin Addis Ababan kasar Habasha. Ginin cibiyar na da fadin kusan sakwaya mita 40,000, cikin fadin filin da ya kai sakwaya mita 90,000. Ana kuma fatan kammala ta a karshen watan Disamban bana. (Saminu Alhassan)