logo

HAUSA

Tashar sararin samaniyar Sin za ta kasance “gida cikin sararin samaniya” ga dukkanin bil Adama

2022-11-01 11:00:36 CMG Hausa

Da misalin karfe 3 da minti 37 na yammacin jiya Litinin 31 ga watan Oktoba, kasar Sin ta yi nasarar harba bangare na uku, na tashar binciken sararin samaniyarta da ake kira Mengtian zuwa sararin samaniya. Sa’an nan, bayan kimanin minti 8, dakin gwaje-gwaje na Mengtian ya rabu da rokar Long March-5B, ya kuma shiga hanyarsa kamar yadda aka tsara. Lamarin da ya nuna cewa, yawan dakunan gwaje-gwaje na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, sun karu daga guda biyu zuwa guda uku, wadanda za su kasance tamkar “siffar T”, matakin dake kara kusanto ga aikin kammala tashar.

Aikin gina tashar binciken sararin samaniyar ya kasance muhimmin mataki a aikin sararin samaniyar kasar Sin, inda kasar Sin ke tsayawa tsayin daka wajen raya aikin bisa manufofin amfani da albarkatun sararin samaniya ta hanyar zaman lafiya, da nuna adalci don cimma moriyar juna, da kuma bunkasa harkokin dake da nasaba da hakan cikin hadin gwiwa.

Kana, cikin tarihin bil Adama, tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ita ce tasha ta farko da aka bude ga dukkanin mambobin MDD. A halin yanzu, kasar Sin ta bayar da izinin yin gwaje-gwaje a tasharta ga shirye-shirye guda 9, da kasashe guda 17, da kamfanoni guda 23. Lamarin da ya nuna aniyar kasar Sin ta inganta dunkulewar dukkanin bil Adama a fannin habaka aikin sararin samaniya.

Albarkatun sararin samaniya sun zama albarkatu ga dukkanin bil Adama, ya kamata a yi amfani da su wajen tallafawa dukkanin bil Adama. Bayan an kammala aikin gina tashar binciken sararin samaniyar kasar Sin, za a shiga matakin amfani, da kuma raya tashar na tsawon shekaru 10. Kana, kafin karshen shekarar bana, kasar Sin za ta kuma harba kumbo mai dauke da kayayyaki na Tianzhou mai lamba 5, da kumbo mai dauke da mutane na Shenzhou mai lamba 15, ta yadda ’yan sama jannati guda 6 za su yi aiki tare cikin tashar.

Ana da imanin cewa, a nan gaba, tashar binciken sararin samaniyar kasar Sin za ta kasance “sabon gida cikin sararin samaniya” ga dukkanin bil Adama, inda za su gudanar da aikin binciken sararin samaniya cikin hadin gwiwa. Cikin tashar, ’yan sama jannati na kasar Sin da na kasashen waje, za su ba da gudummawar binciken sararin samaniya cikin hadin gwiwa, yayin da ake karfafa aikin yin amfani da albarkatun sararin samaniya cikin lumana. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)