logo

HAUSA

Shugaba Xi ya gabatar da lambar karramawa ta abota ga shugaban jam’iyyar CPV ta Vietnam

2022-11-01 11:05:43 CMG Hausa



Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya baiwa babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Vietnam Nguyen Phu Trong, lambar karramawa ta abota.

An gabatar da lambar girmamawar ta jamhuriyar jama’ar kasar Sin ne ga Nguyen Phu Trong a jiya Litinin, a zauren taruwar jama’a dake birnin Beijing, kuma babban dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ne ya karanta kudurin lambar yabon.

Shugaba Xi Jinping ya jinjinawa Trong, a matsayin cikakken mai bin akidun Markisanci, kuma abokin tafiyar JKS na gaskiya.

A nasa bangare, Trong ya godewa shugaba Xi da wannan karramawa, wadda a cewarsa ke kara tabbatar da ma’anar kaunar da JKS, da gwamnati da ma daukacin al’ummar kasar Sin ke nunawa jam’iyyar kwaminis ta CPV, da gwamnati da al’ummar Vietnam, da ma jagororin kasar baki daya. Ya kuma kara da cewa, hakan zai kara zaburar da dadadden kwazon da Vietnam ke yi na karfafa kawancenta da kasar Sin.  (Saminu Alhassan)