logo

HAUSA

An bude zaman farko na majalissar PAP ta 6 a Johannesburg

2022-11-01 11:08:07 CMG Hausa

 

'Yan majalissar dokokin dandalin raya nahiyar Afirka ko PAP ta 6, sun bude zaman farko a jiya Litinin a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu, tare da rantsar da sabbin mambobi. Yayin zaman, shugaban majalissar Fortune Charumbira ya gabatar da jawabin bude taron.

Cikin jawabin nasa, Mr. Charumbira ya ce nahiyar Afirka na fuskantar manyan kalubale da suka hada da yakin basasa, da sauya gwamnatoci ba bisa ka’ida ba, da kamfar abinci, da talauci, da yunwa, da karuwar rikicin makamashi da bala’u daga indallahi. Don haka ya yi kira ga daukacin kasashen nahiyar da su kara azamar shawo kan wadannan matsaloli.

Mr. Charumbira ya ce "Muna kira da a kawo karshen jin amon bindiga, a dakile barkewar tashe-tashen hankula, da rashin tsaro a gabashin janhiruyar dimokuradiyyar Congo, da Somaliya, da arewacin Mozambique, ta hanyar shawarwari tsakanin masu ruwa da tsaki, da aiwatar da ayyuka da suka dace, tare da magance aikata munanan laifuka.”

Kaza lika jam’in ya bukaci kasashen Afirka, da ba su sanya hannu kan yarjejeniyar yankin cinikayya cikin ’yanci ta Afirka ba, da su gaggauta yin hakan. Kana su kawar da harajin cinikayya, da sauran shingaye dake tsakaninsu, ta yadda za a iya bunkasa zirga-zirgar mutane da hajoji tsakanin kasashen shiyyar.

Majalissar dokokin dandalin raya nahiyar Afirka ko PAP, na da jimillar ’yan majalissu 257, wadanda ke zama domin tattauna batutuwan da suka shafi nahiyar Afirka. (Saminu Alhassan)