logo

HAUSA

Yunkurin wasu kasashen yamma na neman bata sunan Sin ba zai yi nasara ba

2022-11-01 19:22:38 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa Talatar nan cewa, kasashen duniya, musamman kasashe masu tasowa da dama, na adawa da siyasantar da batutuwan da suka shafi kiyaye ‘yancin bil-Adam. Sai dai kokarin da wasu kasashen yammacin duniya ke yi na mayar da kasar Sin saniyar ware da ma hana ci gabanta, ta hanyar amfani da irin wadannan batutuwa kamar Xinjiang, ba zai taba yin nasara ba.

Rahotanni na cewa, a ranar 31 ga watan Oktoba agogon wurin, yayin taron kwamiti na uku na babban zauren MDD karo na 77, sama da kasashe 60, sun bayar da sanarwar hadin gwiwa, inda suka yi nuni da cewa, batutuwan da suka shafi Xinjiang, da Hong Kong da Tibet, harkokin cikin kasar Sin ne, kuma suna adawa da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, ta hanyar fakewa da batutuwan kare hakkin bil-Adam.

A game da batutuwan da rahoton dabarun tsaron kasa na kasar Amurka na shekarar 2022 game da kasar Sin da ta fitar kuwa, Zhao Lijian, ya bayyana cewa, da gangan wannan rahoto ya jirkita manufofin harkokin waje da na tsaron kasar Sin, inda a ciki ya bankado aniyar bangaren Amurka na bijiro da wani uzuri da gangan don neman dakile da ma mayar da kasar Sin saniyar ware. (Ibrahim)