logo

HAUSA

Li Keqiang Ya Aikewa Sabon Firaministan Lesotho Sakon Taya Murna

2022-11-01 16:24:16 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya aikewa sabon firaministan kasar Lesotho Sam Matekane sakon taya murnar kama aiki.

Cikin sakon na ranar 28 ga watan Octoban da ya shude, Li Keqiang ya ce Sin na dora muhimmancin gaske ga alakar dake tsakaninta da Lesotho, kuma a shirye take ta yi aiki da bangaren Lesotho, wajen zurfafa amincewar juna ta fuskar siyasa, da fadada kawance, da hadin gwiwa na cimma moriyar juna a fannoni da dama, da ingiza alakar sassan biyu zuwa sabon matsayi, da kuma samarwa al’ummun kasashen biyu moriya.  (Saminu Alhassan)