logo

HAUSA

Shu Qiuhong: Yarinyar dake kokarin sanya mutane mafi yawa su rika sha’awar al'adun gargajiyar kasar Sin

2022-10-31 18:20:03 CMG Hausa

A makon da wuce, mun gabatar muku wata baiwar Allah mai sha’awar saka rigar Han, wato wani nau’in sutura na gargajiyar kabilar Han ta kasar Sin, wadda ta samo asali kimanin shekaru dubu biyar da suka gabata. A makon da ya gabata mun tsaya ne a inda muke bayanin yadda Shu Qiuhong ta soma sha'awar al'adun gargajiyar kasar Sin masu ma’ana da ke tattare da rigar Han. A yau kuma za mu ci gaba daga wannan gaba, a labari mai taken kokarin cimma "Mafarkin rigar Han".

Domin kara mayar da hankali kan sana’arta ta rigar Han, Shu Qiuhong ta yi murabus daga aikin koyarwa. Irin wannan mataki ya gamu da adawa daga iyalinta, har ma mahaifiyarta ta yanke hanyar samun kudin shigar ta.

Matsalolin da ta samu a farkon fara raya sana’a, ba su murkushe Shu Qiuhong ba. Shu Qiuhong da abokiyarta, sun bude wani shago a birnin Ji’nan, hedkwatar lardin Shandong dake gabashin kasar Sin, domin sayar da rigunan Han da wasu kayan aikin hannu.

Ba da dadewa ba, sai aka soma samun yaduwar annobar numfashi ta COVID-19, kuma kusan babu kudin shiga a shagon, Shu Qiuhong ta damu matuka har ta rasa gashin kanta masu yawa. Duk da karin matsalolin da ta fuskanta, amma ba ta yi watsi da sana’arta ta rigar Han ba, Ta yi ta kokari kuma ta yi ta shan aiki, har ma ta kan yi wa ’yan fim salo, da tufatar da su, inda ta haka take iya samun kudin shiga domin ciyar da shagonsu gaba.

A watan Mayu na shekarar 2020, Shu Qiuhong ta zabi gudanar da cinikayya ita kadai. Baya ga daidaita rigunan Han, da yin kwalliya, tana kuma yin kayan kwalliyar gashi ga baki.

Bayan baki sun sanya sofaffin kayan aikin da Shu Qiuhong ta yi da kyalli, da kayan kwalliyar gashi mai salon zomo da take yi da siliki, da ginshikan gashin peony a kansu, gaskiya suna yin kyau sosai, tamkar sun koma lokacin can-can-can da. Sannu a hankali, Shu Qiuhong ta soma shahara a wannan fannin, kuma 'yan uwanta a sana’ar sun amince da kayan adon da take yi da hannu, ta yadda kasuwancin shagonta ya kama hanya madaidaiciya. A ra'ayin Shu Qiuhong, ya kamata mutane su yi abin da suke so a duk rayuwarsu, kuma su yi kokari kan irin abin da suke so.

Abin da ya sa Shu Qiuhong ta nuna farin cikinta shi ne, a cikin 'yan shekarun nan, a karkashin ingantuwa da jagorancin gwamnatin kasar Sin a fannin manufofi, sannu a hankali an shigar da al'adun gargajiya cikin rayuwar mutane ta zamani, kuma "Sha’awa kan nazarin Sinanci", da "Sha’awa kan ayyukan nazari da koyon ilmi" da "Sha’awa kan rigar Han” na kara samun kabuwa a tsakanin Sinawa.

Game da haka, Shu Qiuhong ta bayyana cewa, "Rigar Han ba za ta kasance abun da mutane kalilan ke sha’awa ba." Wannan wata alama ce dake nuna cewa, Sinawa na kara nuna imani kan al'adun kasarsu." A cewarta, bisa la’akari da yadda ake yin hayar rigar Han, da masu neman yin kwaliyya, da daukar hoto a cikin shagonta, da kuma yadda ake sayar da kayan kwalliya iri-iri, ana iya ganin cewa, rigar Han ta soma samun karbuwa a tsakanin mutane kalilan zuwa mutane masu yawa.

Rigar Han tana kuma samun karbuwa a tsakanin abokai na kasashen waje. Shu Qiuhong ta ce, wata yarinya 'yar kasar Rasha ta taba zuwa shagonta ba domin sayen kayan kwalliya ga kanta ba, sai don ta gabatar da kayayyakin dake shagon ga mahaifiyarta a garinsu ta hanyar bidiyo.

Shu Qiuhong ta bayyana cewa, kamar yadda Sinawa su kan ce, “Sanya rigar gargajiyar mu, kuma farfado da kasarmu mai ladabi”. Tana kuma cike da imanin cewa, a nan gaba, mutane da yawa za su yi kaunar rigar Han, watakila kuma za su sanya ta a matsayin rigar yau da kullum, ta yadda za a iya sabunta tufafin gargajiya na kasar Sin da sabbin kuzari a wannan zamani.

A yanzu haka, rigar Han da yadda a ka san ta a tsoffin wakokin, na kara yaduwa a tsakanin matasan kasar Sin, ciki har da Shu Qiuhong.

“Mu yi abubuwan da muke so ko da yake suna da wahala, kuma mu yi iyakacin kokarinmu don wuce matsayin da muke kai a yanzu”, wannan shi ne taken rayuwar matasa masu raya sana’a na kasar Sin, wadanda Shu Qiuhong ke wakilta, a yayin da suke bude sabbin hanyoyi a rayuwa da kuma cimma burinsu.

Rigar Han ba kawai tufafi ba ne, har ma alama ce ta al'adu, ta kasance wani sashe ne na al'adun gargajiya, kuma wani bangare ne na ayyukan farfado da al'adu. Ci gaban kowane abu zai samu karin kuzari idan an shigar da matasa.

Sha’awar rigar Han, ta nuna cewa, al'adun gargajiya na soma samun karbuwa a kasar Sin, kuma Sinawa na kara kwarin gwiwa kan al'adun sannu a hankali. Baya ga haka kuma, matasan kasar dake kokartawa kan makomarsu a nan gaba suna maraba da "zamanin zinare".