logo

HAUSA

Za a kira taron WIC na 2022 a garin Wuzhen daga 9 zuwa 11 ga watan Nuwamba

2022-10-31 14:34:14 CMG Hausa

Za a kira babban taron yanar gizo na kasa da kasa na WIC na shekarar 2022, a garin Wuzhen na kasar Sin daga ranar 9 zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba mai zuwa. Taron na bana dai na da babban taken “Raya sha’anin yanar gizo na duniya cikin hadin gwiwa, a kokarin raya makomar bil Adama ta bai daya ta fuskar yanar gizo”.

Kaza lika taron ya kasance taron shekara shekara na farko da zai gudana, tun bayan kafuwar kungiyar WIC, wanda za a yi fuska da fuska, da ta kafar bidiyo. Ana sa ran wakilai kusan 2000 daga gwamnatoci, kungiyoyin duniya, hukumomin sana’o’i, kamfanonin yanar gizo da kuma jami’o’i na gida da na waje fiye da 120 za su halarci taron, wadanda za su yi cudanyar ra’ayoyinsu bisa babban taken taron, tare da gabatar da dabarunsu game da yadda za a raya makomar bil Adama ta bai daya ta fuskar yanar gizo.

Haka kuma, za a shirya dandalin tattaunawa 20 a yayin taron, don tattauna batutuwan da ke shafar hadin kai da bunkasuwa, da fasaha da sana’a, da al’adu da zamantakewar al’umma, da aikin gudanarwa da kiyaye tsaro. (Kande Gao)