logo

HAUSA

Wang Yi da Blinken sun tattauna ta wayar tarho game da hadin gwiwar Sin da Amurka

2022-10-31 19:23:26 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, da takwaransa na kasar Amurka Antony Blinken, sun tattauna ta wayar tarho Litinin din nan, inda suka yi musayar ra’ayoyi kan hadin gwiwar kasashen biyu wato Sin da Amurka.

A yayin tattaunawar, Wang ya bayyana cewa, dawo da alakar dake tsakanin Sin da Amurka bisa kan turba ba kawai ta dace da moriyar sassan biyu ba, har ma ta dace da muradun kasashen duniya.

A nasa bangare kuwa, Blinken ya bayyana cewa, bangaren Amurka yana fatan ci gaba da yin mu’amala da hadin gwiwa da kasar Sin a mataki na gaba kan huldar dake tsakanin Amurka da Sin, da nazarin tushen hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim)