logo

HAUSA

Ma’aurata Sinawa sun kafa dandalin wasanni da karatu a unguwa don ilmantar da yara

2022-10-31 14:34:06 CMG Hausa


“Muna matukar farin cikin samun wannan karramawa!”cewar Gu Wenzhen, cikin annashuwa, rike da takardar shaidar da aka ba iyalinta na zaman daya daga cikin nagartattun iyalai na kasar Sin na shekarar 2021. Gu da mijinta Wang Xiaojing, sun fito ne daga unguwar Wan’an ta birnin Ningbo a lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin. Sun kafa wani dandalin wasanni da karatu a unguwarsu, kuma suka sanya masa sunan diyarsu, Keke. Iyalin Gu ya samu lambar yabo ne saboda nasarar da ma’auratan suka samu wajen ilmantar da diyarsu.

Gu da Wang ba su san juna ba a lokacin da suke kanana, sai dai, sun taso a yanayi kusan irin daya. Wato sun taso ne a yankunan karkara dake karkashin Huanggang, wani birni a lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin. Baya ga haka, iyayensu ba su samu wani ilimi na a zo a gani ba, amma sun mayar da hankali sosai wajen ba Gu da Wang ilimi. Gu da Wang sun samu kyakkyawan tarbiyya ne daga iyayensu. Wang Xiaojing ya bayyana cewa, “mahaifina ya kan gaya min cewa, bayan wuya sai dadi. Hikimar rayuwa na boye cikin wadannan kalmomi. Iyayena ba masu kudi ba ne a lokacin da nake karami. Sai dai, suna da kwarin gwiwa, kuma sun yi iya kokarin ganin na more lokacin yarintata, abun da ya yi kyakkyawan tasiri kan rayuwata a lokacin da nake tasowa.”

Gu Wenzhen ta kammala karatun digiri na biyu ne a shekarar 2008, a kwalejin nazarin aikin likita ta Tongji ta Jami’ar kimiyya da fasaha ta Huazhong. Ta kuma fara aiki da cibiyar yaki da cututtka ta birnin Ningbo ne bayan ta kammla karatu. Wang Xiaojing kuma ya kammala karatun digirin digirgir ne a shekarar 2010, a jami’ar kimiyya da fasaha ta Huazhong. Yana aiki ne kan tsare-tsare da binciken raya tattalin arzikin bangaren teku a cibiyar nazarin yanayin teku ta Ningbo. Gu da Wang sun yi aure a shekarar 2010, kuma sun samu diyarsu Keke ne shekara guda da aurensu.

Gu ta bayyana cewa, “bayan haihuwar diyata, abubuwa sun yi mana yawa sosai. A wani lokaci idan muka gaji, mu kan kira iyayenmu domin su karfafa mana gwiwa. A ganina, wannan shi ne makasudin iyali.”

A lokacin da Keke take karama, Gu da Wang na yawan kai ta ta yi wasa da sauran yaran dake unguwarsu. “wasa wani muhimmin bangare ne na rayuwar yara kafin su fara zuwa makaranta. Ga galibin iyalai, musammam wadanda ke da yaro guda daya, yana da matukar muhimmanci yaro ya yi wasa da sauran yara yayin da yake tasowa. Yara na kula da juna yayin da suke wasa tare,” cewar Gu.

Gu da Wang sun lura cewa, yara da dama sa’annin Keke, na samun kulawa ne daga kakanninsu. Sai dai, kakannin, saboda tsufa, suna shan wahalar yin wasanni da yaran. Domin shawo kan wannan matsala, a shekarar 2014, Gu da Wang suka tsara wani shiri a unguwarsu ta Wan’an. Sun nemi izini daga kwamitin kula da unguwar domin amfani da dandalin taro na wurin, inda suka gayyaci yara dake unguwar da ma na makwabtan unguwanni domin su yi wasa a dandalin.

Bayan kammala shirin cikin nasara, sai Gu da Wang suka hada gwiwa da unguwar Wan’an wajen kafa wani dandalin wasa, inda suka sanya masa sunan Keke. Wang Xiaojing ya ce, “Makasudin dandalin shi ne, ba yara damar sanin juna, domin inganta fahimta tsakanin iyalai da al’ummominsu, da kira ga iyaye su bayar da kara mayar da hankali ga koyar da ‘ya’yansu.”

Kananan yara a unguwar Wan’an na gudanar da wasannin da dama masu ban sha’awa da iyayen Keke kan shirya a kusan ko wane karshen mako. “Ina gayyatar malamai, wadanda ke da kwarewa a bangaren wake-wake ko fasahohin zane, domin koyar da yaran unguwarmu. Amma abu mafi muhimmanci shi ne, ba yaran damar nishadantuwa da koya daga juna. Wasu yaran, wadanda a baya suke kunya, sun warware kuma suna kara mu’amala da juna,” cewar Wang.

Cikin shekaru 8 da suka gabata, an gayyaci iyayen Keke domin su gabatar da lakca kan ilimin yara kanana a Makarantar Firamare ta gwaji ta Ningbo. Masu sa kai, wadanda ke da kwarewa a harkar ilimin yara kafin su fara zuwa makaranta, sun hada hannu da Gu da Wang wajen inganta dandalin wasanni da karatu da suka kafa. Yayin da suke tattaunawa game da raya dandalin ta yadda zai ci gaba da kasancewa na lokaci mai tsawo, Gu da Wang na fatan karin iyaye za su shiga a dama da su wajen tsarawa yaran shirye-shirye. Haka kuma ma’auratan na fatan gayyatar kwararru kan harkar samar da ilimi daga iyalai, domin kara wayar da kan iyaye game da bukatar inganta ilimin yara. Ta hanyar shirye-shiryen, Gu da Wang na karfafawa iyaye tattauna hanyoyin da ka iya kara inganta bayar da ilimi a gida.

Gu da Wang kan mayar da hankali tare da jajircewa yayin da suke aiki. Amma idan suna wasa da Keke da sauran yaran unguwar, suna sakewa sosai tare da zama cikin annashuwa. Ma’auratan na bayar da matukar muhimmanci ga abubuwan da suke yi. Misali, kowa na tsara lokacin da zai yi aiki ko karatu. Su kan gudanar da ayyukan gida da kansu, kuma da kyau. Duk Juma’a, rana ce ta bayar da labari, inda kowannensu zai bada wani labari da ya karanta ba da jimawa ba. haka kuma, iyalin na shirya liyafa domin murnar bukukuwa. Baya ga haka, Gu da Wang na karfafawa Keke yin tunanin abubuwa da kanta. Su kan nuna mata inda ta yi kuskure tare da karfafa mata gwiwar kara jajircewa. Haka kuma, Keke na gayawa iyayenta abubuwan da take tunanin za su iya yi domin kyautata yadda suke ba ta ilimi.

Samun aboki na da muhimmanci wajen kara fahimtar bukatun yara. Gu da Wang na kasancewa tare da diyarsu ta yadda za su gano yadda za su taimakawa Keke tunkarar matsaloli daban daban. Idan Keke ba ta yi kokari a jarrabawarta ba, za ta fadawa iyayenta cewa, za ta warware matsalarta da kanta.

Gu da Wang sun yi imanin cewa, ya kamata su zamewa diyarsu abun misali. A shekarar 2018, lokacin da unguwarsu ta kaddamar da wani shiri dake da nufin inganta rayuwar mazauna, sai Gu da Wang suka yi aikin sa kai. Sun taimaka wajen wayar da kan mazauna game da rarraba shara, kuma sun koyawa Keke yadda ita ma za ta sauke nauyin dake wuyanta.

Cikin shekarun da suka gabata, Gu da Wang sun hada hannu wajen kokarin yaki da cutar COVID-19. Ko a yanzu, suna zarce lokacin aiki a wuraren da suke aiki ko a cikin unguwarsu. A wani lokaci, Keke kadai ce ke zama a gida. Ta kan tsara yadda za ta yi karatu da kanta, kuma tana iyakar kokarinta wajen tallafawa ayyukan iyayenta. “Idan na girma, ina son bin sahun iyayena, kuma in kara taimakawa karin mabukata,” cewar Keke cike da alfahari. (Kande Gao)