logo

HAUSA

Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar ciki shekaru 65 da kafuwar kungiyar kawancen Rasha da Sin

2022-10-31 14:28:29 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murnar cika shekaru 65 da kafuwar kungiyar kawancen kasashen Rasha da Sin.

Cikin wasikar ta ranar Asabar, shugaba Xi ya ce tun kafuwar kungiyar yau shekaru 65 da suka gabata, tana ta kara azama wajen kyautata cudanya da bangaren Sin, ta kuma bayar da muhimmiyar gudummawa wajen inganta fahimtar juna, da abota, da amincewa juna tsakanin al’ummun kasashen biyu, da ma kara fadada ginshikin tattaunawa tsakanin al’ummunsu. Don haka ya yi fatan kungiyar za ta dore da wannan kyakkyawan aiki nata, na hada kan al’ummun Sin da Rasha.

A daya hannun, shi ma shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya aike da makamancin wannan sako ga kungiyar.  (Saminu Alhassan)