logo

HAUSA

Xi ya isar da sakon jaje ga takwaransa na Koriya ta Kudu kan turmutsutsu da ya faru

2022-10-30 16:06:49 CMG Hausa

A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon jaje ga takwaransa na kasar Koriya ta Kudu Yoon Seok-Youl, sakamakon wani mummunan turmutsutsu da ya auku a birnin Seoul, fadar mulkin kasar.

Cikin sakonsa, shugaba Xi ya bayyana cewa, ya kadu matuka da ya jin labarin faruwar hadarin turmutsutsun, wanda ya hallaka matane da dama. A cewarsa, a madadin gwamnatin kasar Sin da al’ummarta, yana mika ta’aziya ga iyalan wadanda suka rasu, ciki har da wasu Sinawa, kana yana jajantawa iyalan wadanda suka ji rauni, yana kuma fatan Koriya ta Kudu za ta yi iyakacin kokari domin daidaita matsalar yadda ya kamata.

Shi ma firayin ministan kasar Sin Li Keqiang, ya isar da sakon jaje ga takwaransa na Koriya ta Kudu Han Duck-soo a yau. (Jamila)