logo

HAUSA

CMG ya shirya bikin musammam game da “Sabon tafarki na Sin da duniya” a Afirka

2022-10-30 20:11:11 CMG Hausa

A kwanakin nan ne, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin mai kula da Afirka wato CMG Africa, ya gudanar da wasu bukukuwa na musamman kan “Sabon tafarki na kasar Sin da Duniya” a kasashen Kenya da Afirka ta kudu bi da bi.

A yayin taron tattaunawa ta musannan da ya gudana a kasar Kenya kan “Sabon tafarki na kasar Sin da duniya”, jakadan kasar Sin dake Kenya Zhou Pingjian, ya tattauna da editoci da ‘yan jaridu sama da 40 daga kasashen Afirka.

Jakada Zhou Pingjian ya bayyana cewa, kasar Sin tana son kara samar da gudummawar albarkatu ga hadin gwiwar kasa da kasa, da kokarin rage gibin dake tsakanin arewaci da kudanci, da samar da goyon baya da taimako ga kasashe masu tasowa wajen ingiza samun bunkasuwa.

Bugu da kari, an shirya taron karawa juna sani kan “Sabon tafarki na kasar Sin da duniya” a kasar Afirka ta kudu wanda CMG tare da hadin gwiwar jami’ar Johannesburg ta kasar Afirka ta kudu suka dauki nauyin shiryawa tare cikin nasara a birnin Johannesburg. Inda aka gayyaci wakilai da dama daga majalisar dokokin Afirka ta kudu da bangaren gwamnati, da jami’an ilimi domin halartar taron. (Ibrahim)