logo

HAUSA

CMG ya shirya taron yada ruhin taron wakilan JKS karo na 20 a Zanzibar

2022-10-30 15:57:44 CMG Hausa

Cibiyar dake tsara shirye-shirye da harsunan nahiyoyin Asiya da Afirka ta babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG da karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake yankin Zanzibar da hukumar watsa labarai na yankin, sun shirya taron yada ruhin babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 mai taken “Sabon tafarki da makoma ta bai daya” a yankin Zanzibar na kasar Tanzaniya a ranar 26 ga wannan wata, agogon kasar, taron da ya samu halartar babban karamin jakadan kasar Sin dake yankin Zhang Zhisheng, da babbar sakatariyar ma’aikatar kula da watsa labarai da matasa da al’adu da wasannin motsa jiki ta gwamnatin juyin juya hali ta Zanzibar Fatima Hamad Rajab, da shugaban hukumar watsa labarai ta yankin Hassan, da shugabanni da manema labarai na manyan kafofin watsa labarai sama da 20 dake yankin. Yayin taron, wakilan kasar Sin sun yi bayani kan babban sakamako da babbar ma’anar babban taron wakilan JKS karo na 20, da fasahohin da JKS ta samu wajen gudanar da harkokin kasa, duk wadannan sun samu yabo da amincewa daga mahalartan taron.

Babban karamin jakadan kasar Sin dake yankin Zanzibar Zhang Zhisheng shi ma ya gabatar da jawabi yayin taron, inda ya bayyana cewa, kasar Sin wadda ta shiga sabon tafarki na zamanintar da kasa mai bin salon tsarin gurguzu tana son kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da Tanzaniya, domin gina kyakkyawar makomar Sin da Afirka ta bai daya.

Babbar sakatariyar ma’aikatar kula da watsa labarai da matasa da al’adu da wasannin motsa jiki ta gwamnatin juyin juya hali ta Zanzibar Fatima Hamad Rajab ita ma ta yaba wa babban sakamakon da al’ummun Sinawa suka samu karkashin jagorancin JKS, inda ta bayyana cewa, taron da aka shirya zai taimaka wa kafofin watsa labarai na yankin Zanzibar wajen kara fahimtar manufofin tafiyar da harkokin kasa na JKS, haka kuma zai taimakawa kafofin watsa labarai na Zanzibar yayin da suke gabatar da labaran dake shafar kasar Sin, da ingiza hadin gwiwa da cudanya a fannoni daban daban tsakanin sassan biyu wato kasar Sin da Zanzibar. (Jamila)