logo

HAUSA

Xi ya jaddada muhimmancin yada ruhin Yan’an

2022-10-30 16:10:08 CMG Hausa

Kwanan baya babban sakataren kwamitin kolin JKS kana shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran zaunannun mambobin hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS shida, suka tashi daga birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin zuwa birnin Yan’an na lardin Shaanxi, wurin tunawa da juyin juya halin kasar, inda Xi ya jaddada cewa, akwai bukatar a yada ruhin gina JKS na Yan’an, ta yadda za a cimma burin da aka gabatar a yayin babban taron wakilan JKS karo na 20.

Bayan kammala ziyara tasu a Yan’an, Xi ya gabatar da wani muhimmin jawabi, inda ya bayyana cewa, Yan’an muhimmin wuri ne a juyin juya hali na kasar Sin, inda aka yi kokarin kafa sabuwar kasar Sin.

Tun daga shekarar 1935, har zuwa shekarar 1948, kwamitin kolin JKS da Mao Zedong da sauran tsoffin jagoran JKS sun yi rayuwa da kuma yake-yake a Yan’an, inda suka canja makomar kasar Sin a cikin wadannan shekaru 13, ana iya cewa, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta girma ne sakamakon irin da aka shuka a Yan’an, don haka, dole ne a tuna da babbar rawar da Yan’an da mazauna birnin suka taka, kan nasarar babban sha’anin juyin juya hali na kasar Sin. (Jamila)