logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu sanadiyar hare-haren bam da suka tashi a wata mota a Mogadishu ya kai 100

2022-10-30 16:33:28 CMG Hausa

Shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya bayyana cewa, tagwayen bama-bamai da suka fashe a cikin wata mota da aka kai kan wani gini na ma’aikatar ilimin kasar, ya hallaka mutane a kalla 100 kana wasu sama da mutum 300 sun jikkata.

Mohamud ya shaidawa manema labarai, bayan ziyarar da ya kai wurin da aka kai harin bam din yau da safe cewa, mai yiwuwa adadin wadanda lamarin ya shafa ya karu.

Akwai ofisoshin gwamnati da dama da otel-otel, da dakunan cin abinci a kusa da wurin da aka kai harin. 

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan kasar Somaliya Sadiq Dudishe, ya bayyana tun farko cewa, mutane da ba a tantance adadinsu ba, ciki har da ‘yan jaridu da jami’an ‘yan sanda na daga cikin wadanda harin ya rutsa da su.

Kungiyar masu tsattsauran ra’ayi ta al-Shabab mai alaka da al-Qa’ida, wadda galibi ta saba kai hare-hare fadar mulkin kasar da ma iko da galibin sassan kasar, ta dauki alhakin kai harin.

A yayin da yake Allah-wadai da wannan hari, Firaministan kasar Somaliya Hamza Abdi Barre, ya bayyana cewa, irin wannan mataki na kungiyar al-Shabab, ko kadan ba zai taba dakushe kokarin gwamnati na kawar da ayyukan ta’addanci ba. (Ibrahim)