logo

HAUSA

Ruhin Hanyar Ruwa Ta Red Flag Zai Gi Gaba Da Kasancewa Har Abada

2022-10-29 20:32:07 CMG Hausa

A birnin Linzhou na lardin Henan dake tsakiyar kasar Sin, wata hanyar ruwa ta ratsa ta tsaunin Taihang. Hanyar ruwa ta Red Flag, ta kasance aikin samar da ruwa da aka yi a shekarun 1960 domin warware matsalar karancin ruwan sha da ta shafi mutane sama da 500,000. Da safiyar jiya Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci hanyar ruwan, inda ya ce tsarin gurguzu aiki ne da har yanzu ake yinsa, bai tsaya a da can baya kadai ba, yana mai cewa, zai ci gaba har a sabon zamani. (Fa’iza)