logo

HAUSA

Shugaban Nijeriya ya kwantar da hankalin al’umma dangane da batun tsaro

2022-10-29 16:00:27 CMG Hausa

 

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya kwantar da hankalin al’ummar kasar tare da gargadi game da haifar da fargaba ba tare da dalili ba dangane da yanayin tsaro a kasar, yana mai cewa, hukumomin tsaro na aiki ba dare ba rana domin tabbatar da ba su kariya.

Cikin wata sanarwar da aka fitar jiya, shugaba Buhari ya ce, yayin da ake dakile hare-hare, hukumomin tsaron na kokarin magance duk wata barazana da zummar tabbatar da tsaron al’umma, yana mai cewa, galibin ayyukan hukumomin na sirri ne da ba za a iya gani ba.

A farkon wannan mako ne, ofisoshin jakadancin Amurka da Birtaniya dake Nijeriya, suka fitar da wasu shawarwari game da tsaro ga ma’aikatansu, kan yiwuwar aukuwar hare-hare a wuraren taruwar jama’a dake Abuja, babban birnin kasar, inda suka bukaci iyalan ma’aikatan da ba na aikin gaggawa ba, su fice daga kasar ta yammacin Afrika.

Sanarwar ta ce, bai kamata shawarwarin game da tafiye-tafiye da suka fito daga gwamnatocin Amurka da Birtaniya su haifar da fargaba ba, tana mai bayyana yanayin tsaro a matsayin abun dake faruwa a duniya.

Duk da kwashe ma’aikatan da gwamnatocin kasashen wajen suka yi da fargabar da hakan ya haifar, sanarwar ta shugaban Nijeriya ta ce, an dauki karin matakan tsaro a ciki da wajen birnin tarayya Abuja. (Fa’iza Mustapha)