logo

HAUSA

Wurin adana kayan tarihi na shaida al’adun kasa

2022-10-29 19:56:37 CMG Hausa

Wurin adana kayan tarihi na Yinxu na zaune a arewa maso yammacin birnin Anyang dake lardin Henan na kasar Sin, fadin wurin ya kai murabba’in kilomita 30, kuma shi ne wurin adana kayan tarihi na tsohon birnin Sin, wanda ya kasance wurin da aka fi gudanar da bincike kansa, kuma mafi fadi a kasar Sin.

A jiya ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci wannan wuri, inda ya jaddada cewa, al’adun gargajiya na kasar Sin tushe ne na sabon tunanin Jam’iyyar Kwaminis ta Sin, kuma ya kamata a yada al’adu, da kara alfahari da kasar Sin. (Zainab)