logo

HAUSA

Ya kamata bangarori daban daban su yi kokari tare don kiyaye muhallin duniya

2022-10-28 19:46:52 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, kiyaye muhallin duniya, alhakin ne na kasa da kasa, kuma ana bukatar su yi kokari tare, don tinkarar kalubalen yanayin duniya baki daya. Ya ce ya kamata kasashen da suka ci gaba, su sauke nauyin dake wuyansu na rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da cika alkawarinsu yadda ya kamata, da samar da kudi da fasahohi ga kasashe masu tasowa a wannan fanni. Kana kasar Sin za ta ci gaba da hada gwiwa da kasashe masu tasowa a fannin tinkarar sauyin yanayi don samar da gudummawa ga shimfida duniya mai yanayi mai tsabta. (Zainab)