logo

HAUSA

Xi Ya Jaddada Bukatar Inganta Farfado Da Yankunan Karkara

2022-10-28 20:37:20 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar inganta farfado da yankunan karkara ta kowacce fuska, da kokari tukuru domin cimma zamanantar da ayyukan gona da yankunan karkara.

Xi Jinping wanda shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS, kuma shugaban rundunar sojin kasar, ya bayyana haka ne yayin da yake rangadi a birnin Yan’an dake lardin Shaanxi na arewa maso yammacin kasar Sin da birnin Anyang dake lardin Henan, na tsakiyar kasar, daga ranar Laraba zuwa yau Juma’a. (Fa’iza)