logo

HAUSA

Wang Yi ya zanta da takwaransa na Rasha

2022-10-28 11:38:34 CMG Hausa

Babban dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya zanta da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov ta wayar tarho a jiya Alhamis.

Yayin zantawar manyan jami’an biyu, Wang Yi ya ce jim kadan bayan kammalar babban taron wakilan JKS na 20, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya taya babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, murnar kammala taron cikin nasara, wanda hakan ke nuni ga babban matsayin amincewar juna, da goyon baya mai karfi dake tsakanin Sin da Rasha.

Wang, wanda mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya ce Sin a shirye take ta zurfafa musaya da Rasha a dukkanin matakai, da yayata alakar sassan biyu, da daga hadin gwiwar su a fannoni daban daban zuwa sabon matsayi.

A nasa tsokacin, Mr. Lavrov ya taya kasar Sin murnar kammala babban taron wakilan JKS na 20 cikin nasara, tare da taya babban sakatare Xi Jinping murnar sake zabensa. Ya ce taron da ya kammala, babban taro ne mai kima, wanda ko shakka babu zai dora kasar Sin kan turbar cimma babbar manufar farfado da kasa.

Lavrov ya kara da cewa, bangaren Rasha zai inganta cudanya da bangaren Sin a matakai daban daban, da zurfafa hadin gwiwar sassa da dama, da hada karfi da karfe wajen kare zaman lafiya da daidaito a yankin Asiya da Pacific, da ma sauran sassan duniya baki daya.

Bugu da kari, sassan biyu sun yi musayar ra’ayi game da batun Ukraine, da sauran batutuwan da suka shafi kasa da kasa da na shiyyoyi dake jan hankulan su. (Saminu Alhassan)