logo

HAUSA

Cibiyar Africa CDC: Kasashen Afirka 13 sun ba da rahoton bullar annobar kyandar biri

2022-10-28 11:15:15 CMG Hausa

Cibiyar kandagarki da yaki da cututtuka ta Afirka ko “Africa CDC”, ta ce kasashen Afirka 13 sun bayar da rahoton bullar kyandar biri 6,883, daga farkon shekarar nan zuwa yanzu.

Alkaluman da cibiyar ta fitar sun nuna cewa, cutar ta hallaka mutane 173, wato kimanin kaso 2.5 bisa dari na mace-mace da aka samu sakamakon bullarta tsakanin wannan lokaci. Cibiyar ta kara da cewa, cikin jimillar rahotannin bullar cutar 6,883, an tabbatar da harbuwar mutane 891, yayin da aka binciki yiwuwar harbuwar sauran mutum 5,992.

Africa CDC ta bayyana bullar cutar a mataki mai yawa a kasashe 8, da mataki maras yawa a kasashe 5. Kasashen da aka ce cutar na yawaita yaduwa sun hada da Benin, da Kamaru, da Janhuriyar Afirka ta tsakiya, da Congo, Jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Ghana, da Laberiya da Najeriya. Kaza lika kasashen dake da rangwamen yaduwar cutar ta kyandar biri su ne Masar, da Morocco, da Mozambique, da Afirka ta kudu da Sudan.

Tun bayan da hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana kyandar biri a matsayin cutar da ya wajaba duniya ta yi gaggawar maida hankali a kan ta cikin watan Yulin bana, cibiyar Africa CDC ke kira ga kasashen Afirka da su karfafa ayyukan binciken cutar a dakunan gwaje-gwaje, da ma nazarin yanayin kwayoyin cutar domin dakile bazuwarta. (Saminu Alhassan)