Kwallon kafa ta budewa makafi sabon babin rayuwa a Sudan ta kudu
2022-10-27 19:22:26 CMG Hausa
Sanye da kyallen rufe idanu Jimmy Just Augustine, matashi dan kasar Sudan ta kudu mai shekaru 23 a duniya, yana taka leda a kungiyar kwallon kafa ta makafi mai suna “Star Blind”.
Ya kan fafata wasan kwallo tare da sauran abokan wasa, ta amfani da wata nau’in kwallon kafa mai kara da ake wasa da ita, kan ciyawar roba dake shinfide a filin kwallon. Augustine, wanda ke da larurar gani na cikin sabbin ‘yan wasan kwallon kafa dake fatan wakiltar kungiyar, da kasar su, da ma yankin da suke a gasannin kasa da kasa, musamman a wannan gaba da wasan kwallon kafar makafi ke kara samun karbuwa a Sudan ta kudu.
Matashin yana cikin rukunin ‘yan wasa da yawa da aka karrama da lambar kwararru albarkacin ranar “Kare Makafi ta Duniya”, wadda ake bikin ta duk shekara a ranar 15 ga watan Oktoba, da nufin jan hankali don gane da shigar da masu larurar gani cikin harkokin al’umma.
Yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan nan, bayan kungiyar sa ta yi rashin nasara a hannun kungiyar Buluk mai kunshe da masu gani a birnin Juba fadar mulkin Sudan ta Kudu, Augustine ya ce "Ba ma gani da ido, muna amfani da kunnuwan mu domin jin amon kwallo, sai mu bi ta muna bugawa da kafa. Da farko hakan na da wahala, muna yawan buge junan mu, amma yanzu muna iya sarrafa jikin mu muna buga kwallo yadda ya kamata, kana muna iya yin gudu tare da kwallon". Yanzu haka Augustine na cikin matasan Sudan ta kudu masu larurar gani 85, da aka yiwa horo na buga kwallon kafar makafi.
Kwallon kafar makafi an tsara ta ne ta yadda ko wace tawaga za ta kasance mai ‘yan wasa 5, wadanda suke buga kwallo mai kunshe da wasu abubuwa dake kara a cikin ta, ta yadda makafi za su iya gane inda kwallon take su buga da kafafun su. A dukkanin gefen filin kuma an sanya wasu allunan kariya, domin hana kwallon fita daga filin wasa. Kaza lika a kwallon makafi babu dokar satar gida.
A cewar Augustine, "Ina son shaidawa sauran abokan wasa na, da ma daukacin al’umma cewa, nakasa ba gajiyawa ba ce, ko da mutum baya gani da ido, yana iya yin duk abubuwan da masu gani ke yi".
Da yake tsokaci game da rawar da Augustine ke takawa, kocin kungiyar sa Simon Madol Akol, ya ce bayan horas da ‘yan wasa da dama, ciki har da Augustine tun daga shekarar 2020, yanzu haka suna shirin bunkasa wasan kwallon makafi ta yadda zai wuce iya birnin Juba.
Akol ya kara da cewa, "Muna kuma son fadada kwallon makafi zuwa sauran jihohin kasar mu, saboda tuni muka fara fadada bayar da horo zuwa sauran sassan birnin na Juba. Muna fara samar da horo a makarantun kananan yara, saboda mun san cewa wasu daga ‘yan wasan mu na nan suna karatu, kuma ba sa samun damar wasan kwallo tare da takwarorin su masu gani”.
Akol, wanda ya samu horon zama koci ta yanar gizo daga Jamus, ya ce har yanzu ba su yi rajistar kungiyar ‘yan kwallon kafar makafin da gwamnati ba, sai dai kuma yana fatan zai gina wata kungiyar matasa da za ta kai ga wakiltar kasar sa nan gaba a manyan gasanni.
Ya ce "Ya zama wajibi mu samar da wani tsari mai inganci wanda zai zaburar da matasa masu larurar gani su shiga a dama da su sosai a harkar wasanni, hakan ne ya sa muka yi tunanin kwallon kafar makafi. Wasu lokutan idan na fadawa mutane cewa ni kocin kwallon kafar makafi ne sai su yi mamaki. Lallai akwai dokoki na buga wannan kwallo, da farko muna amfani da kunnuwan mu maimakon idanun mu yayin da muke buga kwallo".
Hukumar kwallon kafar turai ta UEFA, da hadin gwiwar gamayyar kungiyoyin kare masu nakasar gani ta duniya ne suka assasa wasan kwallon kafar makafi a Sudan ta Kudu. A yanzu kuma kungiyar masu larurar ido ta Sudan ta kudu ko SSAVI ce ke kula da wasan a kasar.
Wani dan wasa abokin Augustine mai suna Esbon Umbo Jacob, wanda a yanzu ke da shekaru 20 a duniya, wanda kuma ya samu matsalar ido tun yana da shekaru 7 a duniya, ya ce ya zuwa yanzu sun samu kwarewa mai yawa a fannin kwallon makafi, bayan shafe lokaci mai yawa suna buga gasanni.
Esbon Umbo Jacob ya ce "Mun yi nasara a wasanni 2 tun bayan fara buga wasanni. Na farko mun buga shi ne a shekarar 2021, inda muka lashe kofi, wasan yau shi ne na farko da muka yi rashin nasara".
Shi kuwa David Magok, dan shekaru 16 yana da idanu, amma ya sha shiga buga kwallon tare da ‘yan wasan Buluk, tare da sauran kulaflika ciki har da kungiyar Shining star, ya ce kwallon makafi za ta taimaka wajen samar da daidaito da zaman lafiya a Sudan ta Kudu.
Magok ya ce "Ni ina gani, amma shiga ta wasan na da amfani, domin tana bunkasa zaman lafiya a kasa. Yayin da muke wasa tare, muna bunkasa zaman lafiya ta yin hakan.
Kwallon kafar makafi an tsara ta ne da shige irin na kwallon kafa mai ‘yan wasa biyar-biyar, domin amfanar ‘yan kwallo masu larurar ido. A halin yanzu tana cikin wasannin Olympics ajin masu bukatar musamman da ake gudanarwa, kuma hukumar kula da wasannin masu larurar ido ta duniya ko IBSA, na gudanar da gasar cin kofin duniya na wasan.