logo

HAUSA

AIIB ya yi kira da a kara karfafa hadin gwiwa tsakanin shiyyoyi

2022-10-27 10:51:32 CMG Hausa

A jiya Laraba ne aka gudanar da taron shekara shekara, na majalisar bankin zuba jari kan manyan ababen more rayuwar jama’a na Asiya wato AIIB a takaice karo na 7.

Yayin taron wanda ya gudana ta kafar bidiyo, shugaban bankin Jin Liqun ya bayyana cewa, gaba daya adadin jarin da bankinsa ya tattara a cikin shekaru kusan bakwai da suka gabata ya kai dalar Amurka biliyan 85, kuma a nan gaba, zai yi kokarin ingiza hadin gwiwa da cudanya tsakanin shiyyoyi daban daban, ta yadda hakan zai taimakawa kasashe mambobinsa, wajen samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba.

An kafa bankin AIIB ne bisa shawarar kasar Sin, ya kuma fara aiki a watan Janairun shekarar 2016. Yanzu haka annobar cutar COVID-19 tana ci gaba da yaduwa a fadin duniya, a sanadin haka, tattalin arzikin duniya bai samu ci gaba yadda ya kamata ba, don haka Jin Liqun ya yi nuni da cewa, ya dace a kara karfafa hadin gwiwa da cudanya tsakanin shiyyoyi daban daban. A cewarsa: “Makasudin tattara kudade shi ne kyautata rayuwar miliyoyin mutane. A halin da muke ciki yanzu, ya dace mu hada kai, da zamantakewar al’ummun kasa da kasa, domin sa kaimi kan hadin gwiwar dake tsakanin bangarori da dama. A bankinmu, kasar Sin ta bayyana anniyarta ta yin kokari tare da sauran kasashe mambobin bankin, wajen goyon bayan ra’ayin cudanyar bangarori daban daban.” (Jamila)